IQNA

23:54 - May 29, 2020
Lambar Labari: 3484848
Tehran (IQNA) darasin falsafar musulnci da cibiyar musulunci a birnin  Johannesburg ta gabatar ta hanyar yanar gizo a  cikin wata Ramadan ya samu babbar karbuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto daga kasar Afirka ta kudu cewa, darasin falsafar musulnci da cibiyar musulunci da ke birnin  Johannesburg ta gabatar a  cikin wata Ramadan ta hanyar yanar gizo ya samu karbuwa daga sassa na duniya.

Rahoton ya ce an gabatar da darasin a kowace a cikin watan Ramadan mai alfarma, wanda masu bibiyar darasin suke binsa kai tsaye ta hanyar yanar gizo.

Babban abin da darasin ya mayar da hankali a kansa shi ne hikimar addini, da kuma tasirin addini a cikin rayuwar dan adam, da yadda addinin musulnci yake ya kasance ya shafi dukkanin bangarorin rayuwar bil adama da kuma hikimar da ke tattare da hakan.

Mutane dubu 2 da 800 ne daga kasashe 48 suka bi wannan darasi kai tsaye, kuma mutane 242 daga cikinsu duk suna da shedar karatu na digirin digirgir.

Wani mai ban sha’awa shi ne, wadanda suka halarci wannan darasi sun hada da musulmi da kirista da Hindus da kuma yahudawa.

 

3901395

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: