IQNA

Ana Gudanar Da Janazar George Floyd A Garin Minneapolis Na Kasar Amurka

23:42 - June 05, 2020
Lambar Labari: 3484863
Tehran (IQNA) An fara gudanar da janazar gawar George Floyd bakar fata da ‘yan sanda suka kashe a birnin Minneapoli na jihar Minnesota da ke kasar Amurka.

Rahotanni sun ce mutanen da suka halarci jana'izar sun yi tsit na minti takwas da dakika 46, wato adadin lokacin da George Floyd ya shafe a kwance a kasa lokacin da wani dan sanda ya sa gwiwarsa ya danne wuyansa har ya mutu.

An fara gudanar da janazar ne a garin Minneapolis, tare da halartar daruruwan jama’a , inda fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil adama na kasar Amurka, Rebarand Al Sharpton ya gabatar da jawabi mai zafi a wurin taron janazar, inda ya ce yana kiran hukumomin Amurka da su yi adalci kan kisan George Floyd.

Ya ce; Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai an samu sauyi game da tsarin shari'a a kasar Amurka domin lokaci ya yi da za a tashi tsaye, kuma a shelanta cewa; "wannan rashin mutunci ya isa".

Shi ma a nasa bangaren da yake jawabi gaban mahalarta janazar Floyd, lauyansa Benjamin Crump cewa ya yi, ba "annobar corona ce ta yi ajalin George Floyd ba, annobar wariyar launi fata ce ta kashe shi,"

Iyalan Mr Floyd, da Rebarand Jesse Jackson, da gwamnan MinnesotaTim Walz, da dan majalisar dattawan jihar ta Minnesota Sanata Amy Klobuchar da kuma Magajin birnin Minneapolis Jacob Frey suna cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana'izar tasa a North Central University da ke Minneapolis.

Za a kwashe tsawon kwanaki ana gudanar da janazar tasa a garuruwa daban-daban, da suka hada da hada inda aka kashe kashe shi, da kuma inda aka haife shi, da kuma inda ya yi karatu da aiki.

 

 

3903047

 

 

 

captcha