IQNA

UNICEF Ta Ce Yara Fiye Da Mliyan Biyu Ne Suke Fuskantar Yunwa A Yemen

17:53 - June 26, 2020
Lambar Labari: 3484930
Tehran (IQNA) hukumar kula da kananan yara ta duniya ta yi gargadin cewa fiye da yara miliyan biyu ne suke fuskantar yunwa a Yemen.

Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, a halin yanzu akwai yara kimanin miliyan 2.1 da suke fuskantar yunwa  a kasar Yemen, sakamakon yakin kasar take fuskanta.

Babbar jami’ar hukumar UNICEF a kasar Yemen ta sanar da cewa, akwai yiwuwar adadin yara da za su fuskanci amtsananciyar yunwa  aYemen ya kai miliyan 2.4 daga nan zuwa karshen shekara.

Ta ce wannan na faruwa saboda karancin kudade da hukumar take fama da shi, wanda kuma da irin wadannan kudade da kasashen duniya suke bayarwa ne ake gudanar da irin wadannan ayyuka na jin kai musamman na ceto rayuwar kananan yara daga mawuyacin hali.

Bayanin hukumar ya kara da cewa, sun nemi tallafin kudade daga kasashe masu taimakawa domin fusntar wannan matasa da kananan yara suke ciki a Yemen, amma babu wani tallafi na azo a gani da aka samu, inda a halin yanzu abin da ke hannun hukumar Unicef bai wuce kashi 39% na dukkanin abin da take bukata ba domin gudanar da wannan aiki.

Jami’ar hukumar ta idan ba a samu tallafin da ake bukata ba, yara fiye da miliyan biyu da suke fuskantar yunwa  a kasar ta Yemen da dama daga cikinsu za su mutu.

Shekaru biyar kenan a jere Saudiyya tana kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen da sunan yaki da kungiyar Alhuthi, inda dubban fararen hula suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren na jiragen yakin saudiyya, akasarin kuma mata ne da kananan yara.

 

3906955

 

captcha