IQNA

Musawi: Mika Wuya Ba Zai Taba Kawo Tsaro A Yankin Gabas ta Tsakiya Ba

22:49 - June 30, 2020
Lambar Labari: 3484938
Tehran (IQNA) Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Abbas Musawi ne ya bayyana cewa mika wuya ga manufofin Amurka ba zai kawo tsaro a gabas ta tsakiya ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Abbas Musawi ne ya bayyana cewa, babu yadda za a sami tsaro ta hanyar biyayya ga Amurka, yana mai jaddada cewa, hanya daya ta tabbatar da tsaro a cikin wannan yankin shi ne kawo karshen gaba da yin aiki cikin hadin kai

Musawi wanda yake mayarwa da kasashen Saudiyya da Bahrain martani ya ce; Abin mamaki shi ne kasar Saudiyya da ita ce tushen ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a wannan yankin na gabas ta tsakiya, kuma a shekaru masu tsawo ta hargitsa zaman lafiya ta hanyar goyon bayan kungiyoyi irin su al-Qaida da ISIS, ita ce take da bakin da za ta zargi Iran da ta kawo karshen ta’addanci a cikin wannan yankin.

A jiya Litinin ne dai Amurka da Bahrain suka fitar da sanarwa ta hadin gwiwa suna masu yin kira da kada a dauke wa Iran takunkumin hana ta sayar da sayen makamai. Sanarwar tasu ta kunshi zargin Iran da hargiza zaman lafiya a cikin wannan yankin.

 

3907785

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :