IQNA

Falastinawa Suna Gudanar da Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Mamaya

22:57 - July 01, 2020
Lambar Labari: 3484942
Tehran (IQNA) al'ummar falastinu suna gudanar da gangamia yau domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yammacin kogin Jordan.

Shafin yada labarai an I24 ya bayar da rahoton cewa, a yau falastinawa suna gudanar da gangamia yau domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yammacin kogin Jordan da Isra'ila ta sanar da yau a matsayin ranar fara aiwatar ad shirin.

rahoton ya ce an gudanar da wannan zanga-zanga a dukaknin yankuna Falastinawa, da hakan ya hada da yankunan yammacin kogin Jordan, da kuma birnin quds.

Haka nan kuma an gudanar da irinta a dukkanin yankunan zirin gaza, inda dubban mutane suka fito domin nuna rashin amincewa da wannan shiri an Isra'ila.

Fauzi Barhum daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas ya bayyana cewa, babu gudu abbu ja da baya wajen ci gaba da nuna kin amincewarsu da wannan sabon shiri na mulkin mallaka.

3908155

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha