IQNA

Hamas: Sakon Jagora Ya Tabbatar Da Cewa Iran Tana Tare Da Al’ummar Falastinu

23:55 - July 06, 2020
Lambar Labari: 3484958
Tehran (IQNA) Daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas ya tabbatar da cewa sakon jagora manuniya kan matsayar Iran dangane da batun Falastinu.

Tashar Almauadeen ta bayar da rahoton cewa, a zantawarta da Isma’il Ridwan daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas ya tabbatar da cewa sakon jagora manuniya kan matsayar Iran dangane da batun Falastinu da al’ummarta.

Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba za ta taba dakatar da taimako da goyon bayan da take bawa al-ummar Falasdinu wadanda ake zalunta ba.

Jagoran ya bayyana haka ne a jawabin wasikar da shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamsa Isma’ila Haniya ya aiko masa.

Jagoran ya bayyana cewa jajircewar al-ummar Falasdinu musamman kungiyar Hamas a kan tafarkin gwamwarmaya da yahudawa Isara’ila da kuma Amurka ya sanya su debe kauna wajen kara mamayar yankunan al-ummar Falasdinu.

Daga karshe Jagoran ya bukaci al-ummar Falasdinu da ta tabbatar da hadin kai da aiki tare a tsakanin falasdinawa, don hana makiya kutsawa cikinsu don rarrabasu. Idan sun ci gaba da kasancewa a kan abinda suke a kai a halin yanzu, inji jagoran, da yardar Allah yahudawan Sahyoniyya ba za su sake samunta da dadi ba.

 

 

3909066

 

 

captcha