IQNA

Kashi 80% Na Tarjamar Larabci Zuwa Hausa Ta Shafi Addini Ne

19:16 - July 16, 2020
3
Lambar Labari: 3484990
Tehran (IQNA) an gudanar da wani taron karawa juna sani kan tarjamar larabci zuwa a Najeriya tare da halartar masana da kuma malaman jami’ioi.

Jaridar raya ta bayar da rahoton cewa, wannan taro shi ne karo na hudu da ake gudanar da shi a matsayi na kasa da kasa, inda ake yin dubi kan yanayin tarjama da ake yi daga harshen larabci zuwa Hausa.

Dukkanin wadannan suka gabatar da jawabai sun mayar da hankali ne kan irin muhimmancin da harshen Huasa yake da shi a Najeriya da ma sauran kasashen da ake magana da shi, inda ya zama harshe mai hada al’ummomi daban-daban.

A Najeriya akwai al’ummomi da kabilu daban-daban wadanda ba Hausawa ba ne, amma yau da gobe sun wayi gari suna magana da harshen Hausa, a lokaci guda kuma abubuwan da aka rubuta a cikin harshen suna kara samu karbuwa a tsakanin jama’a.

Yahuza Sulaiman Imam daya ne daga cikin mahalrta taron, wanda ya bayyana cewa, bisa bincike da aka gudanar, an iya gano cewa kashi 80 na tarjamar da aka yi daga larabci zuwa Hausa ta shafi addini da kur’ani da fikihu da makantansu ne, yayin da kashi 20 ta shafi adabi da tarihi da wasu ilmomin ne na daban.

Salihu Abubakar Kura, shi ma yana daga cikin mahalarta taron, wanda ya bayyana cewa zamunan da suka gabata an fi yin tarjama ta lafazi a hausa, amma yanzu saboda bunkasar ilimin harshen, ana yin tarjama rubutatta ingantatta bisa ka’idoji na tarjama.

Farfesa Halliru Muhammad abdulbaki ya bayyana cewa, a halin yanzu babban kalubale na tarjama daga larbaci zuwa Hausa yana da alaka da wasu ilmomin larabci ne na adabin harshe, wadanda babu su a Hausa, wanda dole ne mai tarjama ya zama yana cikakkiyar masaniya domin kaucewa fadawa cikin kure.

 

 

3910680

 

Wanda Aka Watsa: 3
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Hasiya
2
7
koyon larabci
Fatima Muhammad
0
2
A gaskiya inason koyon yaren larabci saboda yin magana da mutane saboda zuwa wata kasa wadda ake anfani da yaren sosai ko dai wani taro daza'ayi
Amsoshi
ABDULLAHI KASHURI
TO ALLAH BA MU IKO
captcha