IQNA

Bayanin Majalisar Koli ta Musulmin Najeriya Kan Bukukuwan Babbar Salla

17:27 - July 27, 2020
Lambar Labari: 3485026
Bayanin Majalisar Koli ta Musulmin Najeriya Kan Bukukuwan Babbar Salla
Tehran (IQNA) majalisar koli ta musulmin Najeriya ta fitar da bayani kan halin da ake ciki da kuma yadda ya kamata musulmin kasar su gudanar da bukukuwan salla a cikin irin wannan lokaci.

Shafin punchng ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da majalisar koli ta musulmin Najeriya wato The Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs ta fitar ta bayyana cewa,  bisa la’akari da irin mawuyacin da ake ciki a wannans hekara, musulmi su kauracewa gudunar da manyan taruka a lokacin bukukuwan babbar salla.

Haka nan kuma bayanin ya ce; ganin cewa a shekarar bana maniyya daga Najeriya ba su samu damar tafiya sauke farali ba, a kan hakan mutane za su iya yin amfanin da kudin da suka yi niyyar aikin hajji domin gudanar da ayyukan alhairi da taimakama jama’a marrasa galihu a lokacin idin babbar salla.

Majalisar ta NSCIA ta ce; yanayin da ake ciki yanayi da ba a saba da irinsa ba, a kan haka dole ne a kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya domin kare kai daga kamuwa da cutar corona, ko kuma yada ta ga wasu.

Najeriya dai ita ce kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka baki daya, inda kimanin mutane miliyan dari biyu suke rayuwa a kasar.

 

 

3912865

 

captcha