IQNA

21:19 - August 01, 2020
Lambar Labari: 3485043
Tenran (IQNA) an gabatar da wani shiri na talabijin a kasar Ghana kan sakon jagora Ayatollah Khameni dangane da hajjin bana

A cikin shirin wanda aka gudanar kai tsaye, baki shirin Muhammad Amin Qasim da kuma Mustafa Kuyana, su ne suka tattauna kuma suka fitar da abubuwa na darasi da ke cikin sako, Muhammad Amin Qasim shi ne wanda ya fara gabatar da bayaninsa.

A cikin Karin hasken da ya yi fara ne da dauko batun shi kansa aikin haji tun daga lokacin da annabi Ibrahim yake raya wannan ibada a dakin ka’aba, da kuma yadda aka sanya wanann ya zama daya daga cikin ayyuka na wajibi a kan musulmi.

Ya ce akwai darussa na tarbiya masu tarin yawa a cikin wannan aikin ibada, da hakan ya hada da kaskantar da kai ga ubangiji da kuma mika wuya a gare shi a cikin dukkanin ayyukan wannan ibada.

Baya ga haka kuma akwai darussa na sadaukarwa, wanda kuma ya samo asali ne daga aikin sadaukarwa da annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi ya yi ne a wancan lokaci.

Sannan kuma yace akwai bangare na siyasa, wanad suke yin kure cewa babu siyasa a cikin wannan aiki na ibada, alhali ba haka ba ne, aikin hajji ibada ce da ba a iya rabata da siyasa, domin wuri na haduwar dukkanin musulmi, kuma a nan ne ake isar musu da kowane sako da ya shafi al’umma.

 

 

3913912

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: