IQNA

21:25 - August 02, 2020
Lambar Labari: 3485047
Tehran (IQNA) Sheikh Abdul Amir Qabalan ya kirayi sojojin kasar da su kara zage dantse wajen yin tsayin daga a gaban sojojin Isra’ila da ke yin barazana ga tsaron kasar.

Shafin yada labarai na al’ahad ya bayar da rahoton cewa, a adidai lokacin da sojojin kasar Lebanon suke bikin ranar soji ta kasar, babban malamin mazhabar shi’a a kasar Ayatollah Sheikh Abdul Amir Qabalan ya aike wa rundunar sojin kasar ta Lebanon da sako.

A cikin sakon nasa ya yi jinjina kan irin sadaukarwar da ya ce sojojin kasar suna yi domin kare kasarsu da al’ummarsu, inda ya ce su kara himma a kan wannan manufa ta kare kasa da al’umma daga duk wata barazanar tsaro da Lebanon ke fuskanta daga Isra’ila.

Haka nan kuma malamin ya kirayi dukkanin al’ummar Lebanon da su tsaya sahu guda tare da sojojin kasar tare da mara musu baya, domin su kara samun kwarin gwiwar aiwatar da aikinsu na sadaukarwa.

3914045

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Lebanon ، sojojin ، Sheikh Abdul Amir Qabalan ، fuskanta ، lokacin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: