IQNA

20:44 - August 08, 2020
Lambar Labari: 3485066
Tehran (IQNA) Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da munanan hare-haren da jiragen yakin kasar Saudiyya suka kaddamar a Yemen.

Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da munanan hare-haren da jiragen yakin kasar Saudiyya suka kaddamar kan wasu kauyuka da ke cikin lardin Jauf na kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar fararen hula.

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani a kasar Yemen Martin Griffiths ya bayyana cewa, suna yin tir da wadannan hare-hare na Saudiyya, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula.

A cikin rahoton da majalisar dinkin duniya ta bayar ta sanar da cewa,a  ranar Alhamis da ta gabata, jiragen yakin Saudiyya sun luguden wuta kan gidajen jama’a fararen hula a kauyuk Khob da Sha’ab, inda faren hula 9 suka rasa rayukansu, 7 daga cikinsu kananan yara ne, tare da jikkatar wasu.

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani a kasar Yemen Martin Griffiths ya bayyana cewa, suna kira da a gudanar da binciken gaggawa kan wannan mummunan aiki, wanda ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan fararen hula.

Ita ma a nata bangaren hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya ta fitar da bayani, inda ta yi tir da hare-haren na Saudiyya a kan kananan yara a kasar Yemen, inda ta bayyana hakan da cewa yana a matsayin kisan kiyashi ne a kan kananan yara.

3915314

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen ، Manzon musamman ، majalisar dinkin duniya ، mutuwa ، jikkata ، alhamis
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: