IQNA

22:46 - August 12, 2020
Lambar Labari: 3485079
Tehran (IQNA) ‘Yar majalisar wakilan Amurka musulma Ilhan Omar ta yi nasarar lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyarta a jihar Minneasota a zaben ‘yan majalisar wakilai na kasar da za a gudanar.

Shafin jaridar New York Times ya bayar da rahoton cewa, ‘yar majalisar wakilan Amurka musulma Ilhan Omar, ta samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na fitar dad an takarar jam’iyyar Democrat a mazabarta da ke a jihar Minneasota.

Ilhan dai ta kara ne da abokin hamayyarta a cikin jam’iyyar tasu wato Antone Melton-Meaux, wanda yake da mahanga irin ta Ilhan a wasu bangarori, musamman kare hakkokin bakaken fata da marassa rinjaye a kasar ta Amurka, amma kuma suna da banbanci kan siyasar Isra’ila, inda Ihan Omar take caccakar Isra’ila a kowane lokaci, yayin da shi kuma yake kare manufofin siyasar Isra’ila.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana daga cikin wadanda suke nuna tsananin kiyayya ga Ilhan Omar, saboda ra’yoyinta na siyasa da suka sha banban da nasa, baya ga haka kuma da kasantuwarta musulma ‘yar asalin kasar Somalia.

A cikin watan Nuwamban wannan shekara ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa  akasar ta Amurka, inda a halin yanzu Ihan Omar ta samu tikitin tsayawa takara karkashin inuwar jam’iyyar Democrat.

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wanda ، marassa ، rinjaye ، lashe zaben ، Ilhan Omar ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: