IQNA

22:39 - August 26, 2020
Lambar Labari: 3485121
Tehran (IQNA) shugaban Falastinawa Mahmud Abbs ya bayyana cewa ba ta hanyar kulla alaka da yahudawan Isra'ila ne za a samu hanyar sulhu ba.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, shugaban gwamnatin palasdinawan Mahmud Abbas Abu Mazin, ya hana ministan harkokin wajen Amurkan zuwa ofishinsa dake Ramallah, ya kuma bayyana cewa; “Ba a maraba da shi”

Majiyar ta kara da cewa za a yi wani taro da nufin karfafa alaka tsakanin larabawa da Isra'ila, wanda za a yi a cikin daya daga cikin kasashen larabawan yankin tekun pasha, kuma a halin yanzu Amurka tana kokarin jawo wasu  da su halarci taron.

Majiyar ta kara da cewa; shugaban gwamnatin kwarya-kwaryar Palasdinu Mahmud Abbas Abu Mazin da jami’an gwamnatinsa sun ki amsa goron gayyatar, sannan kuma su ka aike wa da ministan harkokin wajen Amurka da wasikar cewa kada kafarsa ta kata Ramallah, domin ba a maraba da shi.

 

3919059

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: