IQNA

23:25 - August 29, 2020
Lambar Labari: 3485131
Tehran (iqna) magoya bayan Harka Islamiyya a Najeriya sun gudanar da jerin gwano doimn neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Magoya bayan Harka Islamiyya a Najeriya sun gudanar da jerin gwano a birnin Abuja, na neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake ci gaba da tsare shi tare da mai dakinsa Malama Zinat.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama na ciki da wajen Najeriya sun yi ta yin irin wannan kira.

A shekara 2016 ne kotun tarayya a Abuja, ta bayar da umarnin sakin Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa har ma da biyansu diyya, saidai har yanzu ana ci gaba da tsare su.

Wannan dai ba shi ne karon afrko ba da magoya bayaan harkar Islamiyya a Najeriya ke gudanar da irin wanna jerin gwanon na neman a saki shehun malamin nasu da mai dakinsa.

 

3919699

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mai dakinsa ، sheikh zakzaky ، neman sakin ، tsare ، Najeriya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: