IQNA

Masu Kiyayya Da Musulunci Sun Keta Alfarmar Kur’ani Da Yin Batunci Ga Ma'aiki (SAW) A Kasar Norway

21:31 - August 30, 2020
Lambar Labari: 3485135
Tehran (IQNA) masu tsananin adawa da addinin muslunci a kasar Norway sun keta alfarmar kur’ani mai tsarki, tare da yin kalaman batunci a kan manzon Allah (SAW).

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a jiya Asabar wasu gungun masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar Norway sun yi gangami a gaban majalisar dokokin kasar da ke birnin Oslo, inda suka keta shafukan kur’ani mai tsarki.

Shugaban kungiyar masu adawa da musulunci a kasar Norway Lars Thorsen, ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya yi kalaman batunci a kan manzon Allah Muhammad (SAW) wanda hakan ya fusata mutanen da suke adawa da nuna wa musulmi kyama, a nan take suka shiga ba ta kashi a tsakaninsu.

A ranar Juma’a da ta gabata ma wasu masu irin wannan akida ta nuna tsananin kyama ga addinin muslucni a kasar Sewden, sun kona kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki, wanda shi ma ya fusata jama’a da dama, da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi, inda lamarin ya rikide ya koma tashin hankali.

Rasmus Paludan shugaban masu irin wanan akida a kasar Denmark shi ne ya yi kira ga masu irin akidar a kasar Sweden da su gudanar da gangamin kona kur’ani, inda shi da kansa ya yi niyyar halartar gangamin, amma jami’an tsaron kasar Sweden suka hana shi shiga kasar.

3919747

 

captcha