IQNA

An Bude Cibiyoyin Kur’ani A Daga Cikin Jihohin Najeriya

23:16 - September 02, 2020
Lambar Labari: 3485142
Tehran (IQNA) an bude wasu cibiyoyin koyar da kur’ani a cikin jihar Niger da ke tarayyar Najeriya

Shafin yada labarai na Naija 247 News ya bayar da rahoton cewa, Abubakar Bello gwamnan jihar Niger a Najeriya ya sanar da samar da wasu ciboyoyin kur’ani a cikin jihar, wadanda za su taimaka wajen koyar da kananan yara.

Ya ce wadannan cibiyoyin za su rika koyar da yara karatun kur’ani mai tsarki da ma ilimin book na zamani, domin kuwa babban dalilin da yasa aka samar da su shi ne domin a kawo karshen irin halin da yara almajirai suke ciki ne.

Inda gwamnan ya ce akwai yara wadanda shekarun ba su wuce 10 ba wasu ma ba su kai ba, amma suna gararmba akan titi, su ba ga karatun allon ba, kuma bag a na zamani ba, kuma babu wata kulawa, wanda wadannan cibiyoyi za su dauki nauyin kula da su saboda mafi yawa mahaifansu ba su da hali.

Wannan shiri zai kasance  akan wuyan gwamnatin jihar Niger ne, inda za ta rika ware kudade daga cikin da take samu domin tafiyar da wannan cibiya.

 

3920513

 

 

captcha