IQNA

Pakistan Ta Yi Allawadai Da Zanen Batunci Kan Ma'aiki

23:14 - September 03, 2020
Lambar Labari: 3485146
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Pakistan ta yi tir da Allawadai da wallafa zanen batunci a kan manzon Allah (SAW).

Gwamnatin kasar Pakistan ta yi tir da Allawadai da wallafa zanen batunci a kan manzon Allah (SAW) da jaridar kasar Faransa ta yi.

Kmafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta yi, ta bayyana wallafa zanen batuinci ga manzon Allah da jaridar Charlie Hebdo ta kasar ta yi da cewa, yana a matsayin cin zarafin dukkanin musulmi ne na duniya.

Bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakistan ya ce, wallafa irin wannan zane-zane ba ya a matsayin bayyana albarkacin baki ko bayyana ra’ayi, domin kuwa cin mutunci ne a fili ga addini da akida ta wasu daga cikin mutane masu yawa a duniya.

Haka nan kuma bayanin ya kirayi kasashen turai da ake buga irin wadannan abubuwa na cin zarafi ga addinin muslucni a cikinsu da su dauki matakai da suka dace domin hana faruwar hakan, domin al’ummomi su zauna lafiya ba tare da hantarar juna ba.

3920597

 

 

captcha