IQNA

Velayati: Isra'ila Da Wasu Larabawa Na Da Nufin Kawar Da Hankulan Duniya Daga Kan Falastinu

22:37 - September 17, 2020
Lambar Labari: 3485194
Tehran (IQNA) Velayati ya ce manufar kulla alaka tsakanin Isra’ila da wasu larabawa ita ce kawar da hankulan al’ummomin duniya kan Falastin.

Shugaban kwamitin kasa da kasa kan fadakar al’ummar musulmi ya bayyana cewa, manufar kulla alaka tsakanin Isra’ila da kuma masu yi mata amshin shata a cikin larabawa, ita ce kawar da hankulan al’ummomin duniya daga halin da al’ummar falastinu suke ciki.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban babban taron kwamitin kasa da kasa kan fadakar al’ummar musulmi, wanda aka gudanar ta hanyar yanar gizo tare da halartar masana da malamai daga kasashen duniya, shugaban kwamitin Dr. Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa, manufar Isra’ila da kuma larabawan da suka mika mata kai, ita ce kawo karshen duk wani batu na kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta.

Ya ce babban abin kunya da takaici shi ne, yadda wasu daga cikin shugabannin larabawa ne suka zama masu aiwatar da wannan mummunar manufa ta yahudawan sahyuniya a kan al’ummar musulmi da na larabawa.

A ranar Laraba da ta gabata ce gwamnatocin Bahrain da hadaddiyar daular larabawa suka rattaba hannu kan kulla alaka a bayyane tare da gwamnatin yahudawan Isr’ila, yayin da shi kuma firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, wannan nasara ce ga Isra’ila, domin an rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya ba tare da wani sharadi ba, inda ya jaddada cewa Isra’ila za ta ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa tare da gina matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna.

3923446

 

captcha