Wasu majiyoyin diflomasiyya a kasar Sudan sun bayyana cewa, gwamnatocin kasashen Saudiyya da UAE suna ci gaba da yin matsin lamba a kan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan, domin shelanta kulla hulda da Isra’ila, a yunkurin da Donald Trump ke yi na ganin ya samu wani abin kamfe domin yakin neman zabe.
Majiyoyin suka ce kasashen biyu suna yin amfani da mawuyacin halin da Sudan take ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kuma ambaliyar ruwa da ake fama da ita a kasar, domin kwadaitar da ita da biliyoyin daloli, domin ta aiwatar da abin da suke bukata.
Haka nan kuma majiyoyin sun kara da cewa, a yayin wata tattaunawa ta sirri da ta gudana tsakanin firayi ministan riko na kasar Sudan Abdullah hamduk da kuma jami’an gwamnatocin Saudiyya da UAE, Hamduk ya sheda musu cewa, ba zai iya daukar mataki irin wannan ba, saboda abin da kai iya zuwa ya dawo a kasar.
Ko a ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kai kasar Sudan a kwanakin baya, abin da Hamduk ya sheda masa kenan, a lokacin da ya bukace shi da ya shelanta kulla alaka da Isr’ila, saboda masaniyar da Hamduk yake da ita kan cewa, al’ummar kasar ba za su taba amincewa kasarsu ta kulla alaka da Isra’ila ba.
3923745