IQNA

22:41 - September 20, 2020
Lambar Labari: 3485203
Tehran (IQNA) kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya na kasar Iraki ya sanar da cewa, a shekarar bana ‘yan kasashen waje ba za su halarci taron arba’in ba.

Shafin yada labarai na furat News ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da  kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya na kasar Iraki ya bayar ya sanar da cewa, a shekarar bana ‘yan kasashen waje ba za su halarci taron arba’in a Karbala ba.

Bayanin ya ce bisa la’akari da irin halin da ake ciki na yaduwar cutar corona ya zama wajibi a dauki irin wannan mataki, domin dakile yaduwar cutar.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, ‘yan kasar Iraki da suke cikin kasa dole ne su dauki matakai na kariyar kai a dukkanin wurare na tarukan jama’a, da hakan ya hada da masallatai da kuma wuraren hutawa da sauransu.

3924009

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wajibi ، dauki ، halin da ake ciki ، harkokin kiwon lafiya ، Iraki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: