IQNA

Kungiyoyin Fatah Da Hamas Sun Cimma Daidaito Kan Gudanar Da Zabuka A Falastinu

23:21 - September 25, 2020
Lambar Labari: 3485217
Tehran (IQNA) kungiyoyin Fatah da Hamas sun cimma matsaya kan gudanar da zabuka a Falastinu wanda zai hada dukkanin bangarori.

Tashar euro news ta bayar da rahoton cewa, manyan kungiyoyin Falastinawa na Fatah da Hamas sun cimma matsaya kan gudanar da zabuka a Falastinu wanda zai hada dukkanin Falastinawa.

A zanatawarsa da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa, Jibril Rajub babban sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar Fatah ya bayyana cewa, an cimma wannan daidaito ne kan gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki, bayan nan kuma na shugaban Falastinu.

Tun a ranar Talata da ta gabata ce dukkanin bangarorin Falastinawa suka fara gudanar da zama a kasar Turkiya, da nufin sabo bakin zaren warware matsalolinsu na cikin gida domin fuskantar babban kalubalen da ke a gabansu na mamayar kasarsu da yahudawan Isra’ila ke yi.

A shekara ta 2005 ce aka gudanar da zabe, inda Mahmud Abbas Abu Mazin ya lashe zaben a matsayin shugaban Falastinu, wanda ya maye gurbin Malam Yasir Arafat, haka nan kuma taron na Turkiya na da nufin farfado da kungiyar PLO, da nufin sake dawo da manufofin kungiyar na kwantar ‘yancin kai daga mamayar yahudawa.

 

3925177

 

 

 

captcha