IQNA

23:20 - September 27, 2020
Lambar Labari: 3485223
Tehran (IQNA) kungiyar Nujba a kasar Iraki ta bayyana cewa Amurka ce da kanta take da hannu wajen harba makamai a kan ofishinta a Iraki.

Kungiyar gwagwarmaya da ‘yan ta’adda a kasar Iraki ta Nujabaa ta bayyana cewa makamai masu linzamin wadanda ake harbawa kan ofishin jakadancin Amurka a birnin Bagdaza babban birnin kasar, aikin Amurkan ne da kuma wadanda suke mata aiki a cikin kasar.

Babban sakataren Kungiyar Sheikh Akbar Al-Kaabi ya bayyana cewa a wajen kungiyoyi masu gwagwarmaya da ‘yan ta’adda ofisoshin jakadancin kasashen waje a kasar, ba wuraren kaiwa hare-hare ba ne.

 Banda haka suna taimakawa kasar wajen hulda da kasashen waje da kuma samar da ci gaba a kasar.

Ya kara da cewa, hare-haren da ake kaiwa kan wasu wurare kusa da ofishin jakadancin Amurka a birnin Bagdaza aikin mutanen da ita Amurka ta bawa horo ne, don su yi amfani da su wajen bata sunayen kungiyoyi masu gwagwarmaya da ‘yan ta’adda a kasar.

Majalisar dokokin kasar Iraqi dai ta bukaci ficewar sojojin kasashen waje daga kasar ta Iraqi tun farkon wannan shekara.

 

 

3925800

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gwagwarmaya ، Iraki ، ofishin jakadanci ، ci gaba ، makamai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: