IQNA

Taro Mai Taken Gudunmawar Bakaken Fata Musulmi A Turai

22:57 - October 03, 2020
Lambar Labari: 3485239
Tehran (IQNA) an fara gudanar da taro mai taken gudnmawar bakaken fata musulmi a nahiyar turai ta hanyar yanar gizo.

Shafin yada labarai na TRT ya bayar da rahoton cewa, a yau an fara gudanar da taro ta hanyar yanar gizo mai taken gudun mawar da musulmi suka bayar ta fuskoki daban-daban a cikin kasashen duniya.

Wannan taro ana gudanar das hi ne kai tsaye ta hanyar yanar gizo, inda ake gabatar da bayanai daga bakin masana da kuma malamai, dangane da irin kokarin da bakaken fata musulmi suka yi kuma suke yia  bangarori daban-daban na ci gaban al’umma.

Daga cikin har da irin yadda musulmi bakaken fata suka taka rawa tare da bayar da gudunmawa wajen yada ilimin addinin muslunci, inda sau tari akna samu bakaken fata su ne suka fi karbar addinin muslucnia  cikin kasashen turai.

Babbar manufar wannan taro dai ita ce kara karfafa bakaken fata musulmi domin ci gaba da kokarin da suke yi a bangarori daban-daban duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta.

 

3926818

 

 

 

 

captcha