Shafin yada labarai na Palestine ya bayar da rahoton cewa, mutane 1000 ne kawai suka gudanar da sallar Juma’a a yau a masallacin Aqsa da ke birnin quds.
Kwamitin kula da harkokin masallacin quds ya bayyana cewa, yahudawan Isra’ila sun fake da batun corona, inda suka takaida adadin masallata a masalacin aqsa zuwa mutane 1000 kawai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da yahudawan a cikin wannan makon suka bar dubabban yahudawa suka kutsa cikin harabar masallacin da sunan raya idin yahudawa.