IQNA

Shire-Shiyen Sudan Na Kulla Alaka Da Isra’ila

21:34 - October 23, 2020
Lambar Labari: 3485299
Tehran (IQNA) Shugabannin gwamnatin kasar ta Sudan ne su ka tabbatar da cewa Kasar tana gab da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Wani babban jamiín soja na kasar Sudan ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarun cewa; tawagwar Isra’ila da ta Amurka da su ka ziyarci Khartum a makon da ya wuce sun gana ne da jagoran majalisar rikon kwarya kasar Sudan, Abdulfattah Burhan da kuma manyan masu bayar da shawara ga shugaban gwamnati Abdullah Hamduk, dangane da matakai na karshe na kulla alaka da Tel Aviv.

Wani jimiín gwamnatin kasar ta Sudan na daban ya bayyana cewa: Yarjejeniya ta gaba da za a kulla ta kunshi taimako daga Isra’ila da kuma zuba hannun jari, musamman a bangaren fasahar sadarwa da noma a cikin kasar ta Sudan.

Har ila yau, jamiinn na gwamnatin Sudan ya ce; Jamián na gwamnatin Sudan da Isra’ila sun kuma tattauna da kasashen yankin tekun pasha, da kuma wasu na turai hanyoyin da za a yi domin zuba hannun jari a kasar Sudan, da kuma rage musu basussukan da ake bin su.

Bugu da kari majiyar ta ce; A kowance lokaci daga yanzu, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai iya sanar da kulla alaka tsakanin Isra’ila da Sudan.

Ana kuma sa ran cewa Sudan za ta biya Amurka diyyar kudin da suka kai dala miliyan 335 saboda harin da aka kai a ofisoshin jakadancin Amurka a Sudan da Kenya

Wasu rahotanni daga kasar ta Sudan sun bayyana cewar wasu gungun matasa a birnin Khartoum, babban birnin kasar sun gudanar da zanga-zanga don nuna fushi da kuma rashin amincewarsu ga ziyarar da wata tawagar jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kasar a ranar Larabar nan a kokarin da ake yi na kulla alaka tsakanin Sudan da Isra’ilan.

Masu zanga-zangar wadanda suke ta rera taken Allah wadai da gwamnatin ta Sudan, sun kona tutar Isra’ilan don nuna rashin amincewa da kuma kyamarsu ga haramtacciyar kasar, lamarin da ya sanya jami’an tsaro fada musu inda aka ce daya daga cikin masu zanga-zangar ya rasu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon dirar mikiyar da ‘yan sandan suka yi musu.

Wani gidan radion Isra’ilan ne ya sanar da wannan ziyara ta tawagar ta yahudawa, sai dai bai yi karin bayani kan ziyarar da kuma hakikanin manufarta ba, to amma dama a cikin ‘yan kwanakin nan ana ta magana kan kokarin da Amurkawa take yi wajen ganin Sudan ta biyo sahun wasu kasashen larabawan wajen kulla alaka da Isra’ilan.

 

3930835

 

 

captcha