IQNA

Shugaban Faransa Na Ci Gaba Da Shan Martani Daga Al'ummomin Musulmi

22:44 - October 31, 2020
Lambar Labari: 3485325
Tehran (IQNA) duniyar musulmi na ci gaba nuna fushi da kuma tofin Allah tsine ga shugaban kasar Faransa kan goyon bayan da ya nuna ga cin zarafin manzo.

Rahotanni daga bangarori daban-daban na duniya musamman duniyar musulmi suna nuni da cewa al’ummomi da jami’an gwamnatoci daban-daban suna ci gaba da nuna fushi da kuma tofin Allah tsine ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron saboda goyon bayan da ya nuna ga zane-zanen batanci ga Manzon Allah (s.a.w.a) da aka yi a kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Iraki an gudanar da zanga-zangogi a garuruwa daban-daban na kasar don yin Allah wadai da kalaman na Macron inda masu zanga-zangar suka kona tutar kasar Faransa da kuma hotunan shugaba Macron din.

A nan Iran ma cibiyoyi da kungiyoyi daban-daban sun fitar da sanarwar yin Allah wadai da abin a ke faruwa a Faransan kamar yadda kuma jaridun kasar ma sun yi rubuce rubucen yin Allah wadai da wannan danyen aiki da kuma nuna kariya ga Ma’aiki (s.a.w.a) da kuma addinin Musulunci.

A kasar Pakistan kuwa ‘yan majalisar kasar ne, a wani zama da suka gudanar a jiya, suka bukaci gwamnatin kasar da ta kirayi jakadan kasar da ke Faransa da ya dawo gida don nuna rashin amincewarsu.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai ana ci gaba da tofin Allah tsine da kuma kakkausar suka ga kalaman wasu jami’an gwamnatin Faransan musamman shugaban kasar Emmanuel Macron wanda ya nuna goyon bayansa da zanen batanci da cin zarafin da aka yi wa Annabi (s.a.w.a) a kasar da kuma bayyana hakan a matsayin ‘yancin fadin albarkacin baki.

3932247

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shugaban Faransa martani
captcha