IQNA

22:55 - November 04, 2020
1
Lambar Labari: 3485335
Tehran (IQNA) har yanzu dai ana ci gaba da kidaya kuri’un da aka kada a zabukan da aka gudanar jiya a kasar Amurka.

Ana ci gaba da kidaya kuri’un da aka kada a zabukan da aka gudanar jiya a kasar Amurka, inda kuma ake sa ran sanar da sakamakon da zaran an kammala kidaya kuri’un.

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ne dai a kan gaba, da tazara ba mai yawa ba, inda kuma komai zai iya canjawa  a kowane lokaci.

Kwamitin yakin neman zaben Donald Trump ya gabatar da wani taron manema labarai, inda ya sanar da cewa suna da kwarin gwiwa kan lashe zaben ta hanyar samun kuri’u  270 na kwamitocin masu zaben shugaban kasa.

Haka nan kuma shi ma Trump din duk da ikirarin da ya yin a riga malam masallaci wajen cewa ya lashe zaben, amma kuma ya fito ya bayyana cewa, ba zai amince da sakamakon zaben ba matukar dai sakamakon ya nuna cewa ba shi ne ya lashe zaben, inda ya ce zai garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben.

A nasa bangaren dan takarar shugabancin kasar ta Amurka karkashin inuwar jam’iyyar democrat Joe Biden, wanda har zuwa yanzu dai shi ne a gaba bisa kididdigar kuri’un da aka kada, ya bayyana cewa suna da fatar samun nasara, hakan nan kuma kwamitin yakin neman zabensa ya sanar da cewa, nan da wasu ‘yan sa’oi zai gabatar da wani jawabi kai tsaye dangane da batun zaben.

 

3933126

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Balarabe
0
0
ni raayina Allah yaba budin saa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: