IQNA

MDD Ta Kirayi Isra’ila Da Ta Dakatar Da Rushe Gidajen Falastinawa

23:47 - November 06, 2020
Lambar Labari: 3485341
Tehran (IQNA) majalisar dinkin duniya ta bukaci Isra’ila ta dakatar da rushe-rushen gidajen Falasdinawa.

Jakadan MDD na musamman kan kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya bukaci haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta dakatar da rushe-rushen gidajen Falasdinawa a yankunan su da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Spotnik na kasar Rasha ya nakalto Evan Haily ya na fadar haka a ranar Alhamis da dare. Ya kuma kara da cewa a shekara ta 2020 da muke ciki, HKI ta fi rusa gidajen Falasdinawa a baya-bayan nan.

Har’ila yau Stéphane Dujarric kakakin babban sakataren MDD ya bayyana cewa rushe-rushen da HKI ta yi a wannan shekarar a kasar Falasdinu da aka mamaye yana damun majalisar. Don haka ya bukaci HKI da dakatar da hakan.

Rohotannin MDD dai, sun tabbatar da cewa gwamnatin yahudawan Sahyoniyya sun rusa gidajen Falasdiwa 689 a yankin yammacin kogin Jordan da kuma birnin Quds kadai a cikin wannan shekara ta 2020 da muke ciki, inda ta bar Falasdinawa kimani 869 basu da wurin zama.

 

3933487

 

captcha