IQNA

23:52 - November 10, 2020
Lambar Labari: 3485352
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen musulmi ta yi tir da shirin Isra’ila na ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa.

Kamfanin dilalnin labaran SAFA ya bayar da rahoton cewa, a ikin bayanin da ta fitar, kungiyar kasashen musulmi ta yi tir da shirin Isra’ila na ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa tare da gina matsugunnan yahudawa a cikinsu.

Kungiyar ta kirayi sauran kasashen duniya da su sauke nauyin da ya rataya a kansu na takawa Isra’ila burki dangane da cin zalun da take yi a kan al’ummar Falastinu da ta mamaye musu kasa.

Bayanin kungiyar ya ce barin gwamnatin yahudawan Isra’ila tana yin abin da ta ga dama, ba tare da sauran bangarori na kasa da kasa sun taka mata burki ba, zai kara sanya shakku dangane da da’awar adalci da kare hakkokin ‘yan adam da manyan kasashen duniya key i.

A nasa bangaren wakilin Falastinu a kungiyar kasashen musulmi Rayad Mansur ya bayyana cewa, akwai nau’in munafunci da rashin gaskiya dangane da yadda manyan kasashen duniya suke nuna halin ko in kula da irin mawuyacin halin da Isra’ila ta jefa Falastinawa.

 

3934404

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: