IQNA

22:46 - November 19, 2020
Lambar Labari: 3485380
Tehran (IQNA) wani fitaccen mai fasahar rubutun larabci dan kasar Syria ya rubuta cikakken kwafin kur’ani da salon rubutu mai ban sha’awa.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Ahmad Hazim Najib mutum ne mai fasahar rubutun larabci dan kasar Syria wanda ya rubuta cikakken kwafin kur’ani mai tsarki da salon rubutu mai kayatarwa matuka.

Ya bayyana cewa rubutun wannan kur’ani ya dauke shi tsawon shekaru uku a jere yana yi, inda yakan rubuta shafi uku a kowace rana na kur’ani mai tsarki.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, bisa la’akari da cewa yana yin amfani da salon rubutu na fasaha ne mai kayatarwa, yakan dauki sa’a guda ko fiye da hakan a kan rubutun kowane shafi.

 
آماده// کتابت قرآن کریم به دست خطاط سوری + عکس
 
آماده// کتابت قرآن کریم به دست خطاط سوری + عکس

3935956

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: