IQNA

Gwamnatin Burtaniya Ta Kirayi Isra'ila Da Ta Dakatar Da Gine-Gine A Cikin Yankunan Falastinawa

21:37 - November 26, 2020
Lambar Labari: 3485402
Tehran (IQNA) Gwamnatin Burtaniya ta bukaci gwamnatin yahudawan Isra’ila da ta dakatar da shirinta na gina sabbin matsugunnan yahudawa a gabashin birnin Quds.

A cikin wani bayani da mai magana da yawun gwamnatin Burtaniya ya fitar, ya bayyana cewa, gwamnatin Burtaniya ta kirayi gwamnatin Isra’ila da ta dakatar da shirinta na gina sabbin matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Quds.

Ya ce matsayin gwamnatin Burtaniya dangane da batun gina matsugunnan yahudawa a gabashin birnin Quds a bayyane yake, domin kuwa hakan ya sabawa dukkanin dokoki na duniya, wadanda majalisar dinkin duniya ta amince da su.

Wannan dai na daga cikin shirin da gwamnatin Netanyahu take da shi, na ganin ta sake gina wasu sabbin matsugunnan yahuwa dubu daya da 267 a cikin yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Quds, inda aka gabatar da wanann shiri a ranar 16 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki.

Netanyahu ya yi alkawalin aiwatar da wanann shiri, inda yana daga cikin bangaren yarjejeniyar karni da gwamnatin Trump ta bullo das hi, tare da amincewar wasu daga cikin gwamnatocin larabawa, wanda hakan zai hada da mamaye yankunan Falastinawa da yammacin kogin Jordan, domin gina matsugunnan yahudawa a cikinsu.

3937489

 

captcha