IQNA

Bangaren Kula Da Gyaran Tsoffin Takardu Da Littafai Na Hubbaren Hussaini

23:24 - November 27, 2020
Lambar Labari: 3485405
Tehran (IQNA) bangaren kula da gyaran tsoffin littafai da takardu na hubbaren Imam  Hussain na ci gaba da kara bunkasa ayyukansa.

Bangaren yada labarai na hubbaren Imam  Hussain ya bayar da bayanin cewa bangaren kula da gyaran tsoffin littafai da takardu na wanann hubbaren, ya gudanar da wasu ayyukan na gyaran wasu dadaddun takardu da aka rubuta da hannu, da suke dauke da ilmomi na addini.

Bayanin ya ce, wannan cibiya tana gudanar da ayyukanta ne tare da hadin gwiwa da cibiyoyin bincike na jami’ioi daban-daban na ciki da wajen kasar Iraki.

Tun daga shekara ta 2005 da aka kafa wannan cibiya, ya zuwa ta gyara takardu da littafai wadanda sun rududduge, wadanda adadinsu ya kai dubu 5 da 500, ta hanyar yin nazari mai zurfi da bin diddigin abin da aka rubuta.

 

3937660

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha