IQNA

22:25 - November 28, 2020
Lambar Labari: 3485410
Tehran (IQNA) ana ci gaba da mayar da martani a duniya dangane da kisan gillar da aka yi wa babban masanin ilimin nukiliya na kasar Iran a jiya.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa masanin nukiliya dan kasar Iran a jiya Juma’a.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, Farhan Haq mai magana da yawun babban sakataren majalisar ya fadi yau cewa, Antonio Guterres ya nuna damuwarsa matuka kan kisan da aka yi wa masanin nukiliya dan kasar Iran, tare da yin kira da a kwantar da hankula domin kada hakan ya kai ga jefa yankin gabas ta tsakiya cikin wani sabon rikici.

A nata bangaren gwamnatin kasar Rasha ta bayyana kisan Mohsen Fakhrizadeh da cewa akwai hannun Amurka dumu-dumu a cikin lamarin, kuma wannan wani mataki ne da ake nufin cimma wata manufa ta siyasa da shi.

Ita ma ‘yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Omar, tare da tsohon daraktan hukumar leken asiri ta Amurka John Brennan, sun bayyana kisan Fakhrizadeh da cewa laifi ne, domin kuwa babu wani dalili kan cewa mutumin da aka kashe yana tattare da wani hadari.

A nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta fitar da bayani, wanda a ciki ta yi Allawadai da kisan da aka yi wa Fakhrizadeha  jiya a kusa da birnin Tehran, tare da bayyana hakan da cewa ya yi hannun riga da siyasar kungiyar tarayyar turai, da dokoki na hakkin dan adam na duniya.

Gwamnatocin kasashen duniya daban-daban sun yi Allawadai da wanann aiki, kamar yadda kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasashen musulmi da na larabawa da dama sun yi Allawadai da wannan kisa, tare da zargin Amurka da yahudawan Isra’ila, da hannun kai tsaye a cikin hakan.

Baya ga haka kuma wasu daga cikin kungiyoyin gwagwarmaya  a yankin gabas ta tsakiya sun bayyana cewa,a  saurari martani kan Amurka da Isra’ila dangane da wannan ta’asa da suka aikata tare da ‘yan korensu daga cikin shugabannin kasashe masu munafurtar musulmi da cin amanarsu a yankin.

3937720

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: