Babban manzon majalisar dinkin duniya a kasar Yemen Martin Griffith ya bayyana cewa, lokaci da ya kamata a kawo karshen yakin kasar Yemen, ta hanyar samun fahimtar juna tsakanin dukkanin bangarorin siyasar kasar kasar.
Ya ce yana da kyau bangarorin siyasar da suka hada da gwamnatin Hadi Mansur da kuma gwamnatin San’a karkashin jagorancin Ansarullah, su koma kan teburin tattaunawa, su samar da hanya guda ta sulhu da warware matsalolinsu.
Manzon majlaisar dinkin duniya ya kara da cewa, al’ummar Yemen ne kawai a tsakaninsu za su iya warware matsalolinsu na siyasa, ba tare da shigar shugula ta kasashen ketare ba.
Haka nan kuma ya kara da cewa, a shirye yake domin ya ci gaba da aikin sasanta bangarori na kasar Yemen, domin samun zaman lafiya dorewa a kasar daga shekara mai kamawa, domin kuwa a shekara mai karewa babu abin da aka gani kasar sai kisa da yunwa da corona da kuma gudun hijira.
Ofishin majalisar dinkin duniya kan harkokin agaji ya bayar da rahoton cewa, daga lokacin da kasar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare a kan kasar Yemen a 2014, ya zuwa mutane dubu 233 ne suka rasa rayukansu a kasar.