IQNA

Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Bayan Tashin Wasu Bama-Bama A Filin Jirgin Aden Yamen

22:59 - December 30, 2020
Lambar Labari: 3485508
Tehran (IQNA) wasu bama-bamai sun tashi a lokacin da ministocin gwamnatin Mansur Hadi ke isowa filin sauka da tashin jiragen sama da ke birnin Aden a kudancin Yemen.

An tashi wasu abubuwa masu matsananciyar kara wajen fashewa a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Aden a kudancin kasar Yemen.

Rahoton ya ce lamarin ya auku ne a daidai lokacin da tawagar ministocin gwamnatin Mansur Hadi da ke da matsugunni a birnin Riyad na kasar Saudiyya, take isowa filin jirgin daga Riyad.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da takun saka yake ta kara kamari tsakanin bangarorin da suke mara baya ga kawancen da ke kaddamar da yaki kan kasar ta Yemen, inda bangarorin dazaman  ke samun goyon bayan Saudiyya da suka hada da bangaren Hadi Mansur, suke zaman doya da manja da bangarorin da ke samun goyon bayan hadaddiyar daular larabawa.

Sai dai faruwar lamarin ke da wuya, sai gwamnatin Hadi ta zargi kungiyar Ansarullah (Alhuthi) da cewa ita ce ta kai harin, yayin da ita kuma kungiyar ta bayyana cewa ba ta hannu a cikin lamarin, ta da bayyana cewa hakan wata manuniya ce kan babban sabanin da ke tsakanin bangarorin da suke yaki da al’ummar kasar, inda suka fara kashe junansu ba tare da rahma ba.

An yi ta jin barin wuta bayan tashin bama-baman a cikin filin jirgin, tsakanin dakarun Hadi da kuma wasu da basa ga maciji da juna da su a cikin masu mara baya ga kawancen yaki da kasar Yemen.

3944541

 

 

 

captcha