IQNA

Hassan Bitmez: Sulaimani NE Ya Hana Aiwatar Da Manufofin Yahudawa A Gabas Ta Tsakiya

22:34 - January 09, 2021
Lambar Labari: 3485539
Tehran (IQNA) mataiamkin shugaban jam’iyyar Saadat a kasar Turkiya ya bayyana cewa, Kasim Sulaimani ne ya hana aiwatar da shirin yahudawa sahyuniya a gabas ta tsakiya.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, mataiamkin shugaban jam’iyyar Saadat a kasar Turkiya ya bayyana cewa, Kasim Sulaimani ne ya zama babban karfe kafa wajen hana aiwatar da shirin yahudawa sahyuniya a gabas ta tsakiya baki daya.

Ya ce kisan Kasim Sulaimani ba abu ne da ya auku ba tare da lissafi ba, shi ne wanda ya hudawa suke da shi da jimawa, kuma gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Trump ta aiwatar musu da shi.

Akwai dalilai da dama da suka sanya yahudawan sahyuniya daukar wannan mataki a kan Sulaimani, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne, ya zama babban karfe kafa wajen hana su cimma bakaken manufofinsu a kan kasashen yankin gabas ta tsakiya.

Babban abin da ya kara bakanta ran yahudawan Sahyuniya dangane da batun Kasim Sulaimani shi ne, yadda ya ragargaza ‘yan ta’addan Daesh a cikin Syria da Iraki, wadanda aka yi amfani da su domin rusa wadannan manyan kasashen musulmi biyu.

Hassan Bitmez ya ce, wani babban abin bakin ciki shi ne yadda wasu daga cikin shugabanni da sarakuna na larabawa suka zama ‘yan amshin shata na yahudawa, baya ga haka kuma sun zama su ne karnukan farautar da yahudawan suke yin amfani su domin wannan mummunar manufa ta su a kan musulmi da ma larabawa.

Baya ga haka kuma, majalisar dinkin duniya da manyan bangarori na kare hakkin bil adama na kasa da kasa, duk sun zama karkashin ikon yahudawa ne, ta yadda ba za su iya tabuka komai ba, sai abin da yahudawan suka yarje musu.

Mataiamkin shugaban jam’iyyar Saadat ya bayyana cewa, Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas ya kira Kasim Sulaimani da sunan shahidin masallacin Quds, domin kuwa ya bayar da dukkanin gudunmawa wajen taimakon al’ummar Falastinu domin gwagwarmayar ‘yantar da masallacin Quds mai alfarma daga mamayar yahudawa.

Ya ce amma shi zai kira Kasim Sulaimani da sunan shahidin musulunci, domin dukkanin rayuwarsa ya karar da ita ne wajen hidima ga addini da taimakon musulmi da ake zalunta a duniya, kuma akan wannan tafarki ya rasa rayuwarsa.

3946136

 

 

 

 

captcha