IQNA

Shirin Bayar Da Horo Kan Ilmomin Kur’ani Ta Hanyar Yanar Gizo

22:49 - January 10, 2021
Lambar Labari: 3485542
Tehran (IQNA) shirin bayar da horo kan kan ilmomin kur’ani na cibiyar kur’ani ta kasar Burtaniya ta hanyar yanar gizo zai fara gudana nan da mako guda.

Cibiyar kur’ani ta kasar Burtaniya ta bayar da bayanin cewa, malaman kur’ani na cibiyar za su jagoranci shirin bayar da horo kan ilmomin kur’ani da aka fara a shekarar da ta gabata ta hanyar yanar gizo.

Wadanda za su halarci wannan horo dai sun fito ne daga kasashen Burtaniya, Canada, Amurka, Faransa, Kenya, tanzani da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Za a fara gudanar da shirin ne daga ranar 18 ga wannan wata na janairu har zuwa tsawon watanni uku a jere.

Muhimman abubuwan da horon zai mayar da hankali a kansu shi ne, bayani kan ayoyin kur’ani mai tsarki da suke magana a kan abubuwa da suka shafi rayuwar dan adam ta fuskokin siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da kuma ‘yan adamtaka.

Wadanda suke da sha’awar ziyartar shafin yanar gizo na cibiyar kur’ani ta burtaniya, za su shiga ta wanann adireshi:

https://lms.darulquran.co.uk/en

3946702

 

captcha