IQNA

Masar Ta Bayar Da Kwafin Kur’ani 200 Tarjamar Harshen Indonesia Ga Ofishin Jakadancin Kasar

21:55 - January 12, 2021
Lambar Labari: 3485548
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Masar ta bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen Indonesia ga ofishin jakadancin kasar.

Shafin yada labarai na Almisrawi ya bayar da rahoton cewa, a jiya gwamnatin kasar Masar ta bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki guda 200 da aka tarjama a cikin harshen Indonesia ga ofishin jakadancin kasar ta Indonesia da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar.

Ofishin jakadancin kasar ta Indonesia wanda yake daukar nauyin dalibai 75 dukkaninsu ‘yan kasar Indonesia da suke karatu a jami’ar Azhar, ya bayar da wadannan kwafin kur’anai ga kowanne daga cikinsu, kamar yadda kuma sauran za a aike da su zuwa ga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

A shekarar da ta gabata ce babban kwamitin koli na kula da harkokin addinin muslunci a kasar Masar ya bayar da aikin tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harsuna 10, wato turancin Ingishi, Faransanci, Jamusanci, Rashanci, China, Esfaniyanci, Swahili, harshen Koriya da kuma Albania.

Babbar manufar hakan dai ita ce yada koyarwar kur’ani a cikin harsuna daban-daban ga al’ummomin duniya, domin su karanta shi da yarensu kuma fahimci zancen Allah madaukakin sarki kamar yadda yake.

 

3947084

 

 

captcha