IQNA

Karamar Yarinya Mahardaciyar Kur’ani Wadda Kuma Ta Zo Ta Daya A Gasar Lissafi Ta Duniya

21:50 - January 13, 2021
Lambar Labari: 3485550
Tehran (IQNA) wata karamar yarinya ‘yar shekaru 8 da haihuwa mai kaifin basira baya ga hardace kur’ani tana kuma karfin fahimtar lissafi.

Tashar Aljazeerah ta bayar da rahoton cewa, yarinyar mai suna Sarah Kiyali an haife ta a yankin Idlib na kasar Syria, inda lamarinta yake da matukar ban mamaki ga kowa.

Wannan karamar yarinya ta nuna baiwar da Allah ya yi mata a gasar kwakwalwa ta duniya ta ACIDA, wadda kasar China ta dauki nauyin shiryawa, inda ta zo ta daya a dukkanin bangarorin da gasar ta kunsa na lissafi, a tsakanin yara fiye da 6000 da suka shiga gasar daga kasashen duniya daban-daban.

Sarah ta bayyana cewa tana son ta zama malamar lissafi a rayuwarta, domin ta bayar da gudunmawa ga al’ummar kasarta a wannan bangare.

3947473

 

 

 

captcha