IQNA

Fitaccen Makarancin Kur’ani Na Duniya Marigayi Muhammad Siddiq Minshawi

23:41 - January 20, 2021
Lambar Labari: 3485572
Tehran (IQNA) a yau ne aka cika cika shekaru dari da daya da haihuwar  fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki da ya shahara a duniya Muhammad Siddiq Minshawi.

Muhammad Siddiq Minshawi fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki ne da ya shahara a duniya, wada kuma sunansa ya dawwama a cikin makaranta littafin ubangiji mai tsarki.

An haife shi a ranar 20 ga watan Janairun 1920, wato yau shekaru 101 cif da haihuwarsa a kasar Masar.

Tun yana dan shkaru 8 da haihuwa ya hardace kur’ani mai tsarki, yana dan shekaru 9 ya fara halartar taruka domin gabatar da karatun kur’ani tare da mahaifinsa.

A cikin kan kanin lokaci sunan Muhammad Siddiq Minshawi ya yadu a kasar Masar da ma kasashen larabawa, inda karatunsa ya zama daga cikin karatuttukan da ake sakawa a gidan radiyo a lokacin.

Ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya domin gabatar da karatun kur’ani a manyan taruka, daga cikin kasashen Indonesia, Libya, Palestine, Jordan, Kuwait, Saudiyya, Syria, Iraki, Pakistan, Morocco, Sudan.

A shekara ta 1955 sun yi tafiya tare da babban makaranci Abdulbasit Abdulsamad zuwa kasar Indonesia, a cikin 1966 ya tafi Baghdad, sai kuma a 1969 tare da sheikh Khalil Alhusari sun tafi Libya, a cikin wannan shekarar nea  ranar 20 ga watan Yuni ya rasu a birnin Alkahira yana da shekaru 49 a duniya.

3948722

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :