IQNA

Biden Ya Fara Da Soke Wasu Dokoki Da Trump Ya Kafa

21:03 - January 21, 2021
Lambar Labari: 3485575
Tehran (IQNA) Sabon shugaban Amurka, Joe Biden, ya sanya hannu kan wasu sabbin dokoki sa’o’i kadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 46 a jiya Laraba.

Wasu daga cikin kudurorin da M. Biden ya sanya wa hannu, sun yi hannun-riga da manufofin tsohon shugaban kasar Donald Trump.

Daga cikin dokokin akwai shirin sanya kafar wando guda da annobar korona, da dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, da fige da fice da dakatar da gina Katanga tsakanin iyakar kasar da Mexico.

Sabon shugaban Amurkar ya soke dokokin da ke hana ‘yan wasu kasashen musulmi da wasu na Afirka shiga Amurka.

Joe Biden ya kuma sauya tsauraran matakan da aka dauka tsawon shekaru hudu, kan zama dan kasa a Amurka.

A jiya ne dai aka rantsar da Biden, a matsayin sabon shugaban kasar ta Amurka.

Baya ga Biden kuma an rantsar da Kamala Harris, a matsayin mataimakiyarsa, wacce ita ce mace ta farko kana kuma bakar fata da ta fara rike wannan mukami a tarihin Amurka.

3949006

 

 

 

captcha