IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allawadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai A Iraki

22:38 - January 22, 2021
Lambar Labari: 3485578
Tehran (IQNA) majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da harin ta’addancin na kunar bakin wake da aka kai a birnin Bagadaza na kasar Iraki a jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya kan harkokin Iraki Jenin Hennis Plaschart ta yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai a birnin Bagadaza na kasar Iraki a jiya Alhamis, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 32 dukkaninsu fararen hula, tare da jikkatar wasu da dama.

Jenin Hennis Plaschart ta ce abin da ya faru a Iraki a jiya abin bakin ciki ne matuka da yake daga hankali, musamman ganin cewa lamarin ya faru ne a cikin jama’a kuma har ya jawo asarar rayuka.

Ta ce al’ummar Iraki suna da masaniya kan nau’oin zalunci da suka gani tsawon shekaru a gwamnatocin da suka gabata a kasar, amma da juriyarsu da hakurinsu hakan ya zama labari, kamar yadda kuma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan ma sun ga ayyuka na ta’addanci iri-iri kuma aka shawo kansu.

Ta ce tana kira ga dullanin bangarori na al’ummar kasar, yan siyasa da malamai da shugabannin kabilu da mahukunta da jami’an tsaro, da su kara hada karfi da  karfe domin tunkarar duk wata barazana a kan kasarsu.

Kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kai harin na jiya a birnin Bagadaza, kuma mutane biyu da suka tarwatsa kansu da bama-bamai a wannan hari dukkaninsu ‘yan kasar Saudiyya mambobi a kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh.

3949162

 

captcha