Shafin yada labarai na Albawwaba News ya bayar da rahoton cewa, babban baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanawa yanzu haka a wani bangaren ajiye kayan tarihi dake cikin masallacin manzon Allah (SAW) birnin Madina,yana samu karbuwa daga dubban maziyarta.
Rahoton ya ce a wurin wannan baje koli ana nuna nau’oin kwafin kur’anai da aka buga da inji da kuma wadanda aka rubuta su da hannu.
Tarihin rubutun wadannan kur’anan yana komawa zuwa ga lokuta daban-daban, wasu daruruwan shekaru, wasu kuma gomomin shekaru, daga ciki kuma akwai kwafin kur’anai da suke komawa tun shekaru fiye da dubu da suka gabata.
Tun a shekaru hudu da suka gabata ne aka fara gudanar da wannan baje kolin a bangaren ajiye kayan tarihi da ke cikin masallacin ma’aiki, wanda wasu malamai masu tsatsauran ra’ayi a kasar ta Saudiyya suka haramta hakan bisa hujjar cewa yin hakan bai zo a cikin sunna ba, amma duk da haka dai an ci gaba da gudanar da baje kolin na kur’ani, tare da izinin gwamnatin kasar.