Tashar Al-shuruq ta bayar da rahoton cewa, a yau Litinin an fara gudanar da gasar kur’ani ta duniya ta yankin Port Saeed a kasar Masar tare da halartar malamai da kuma alkalan gasar gami da makaranta da mahardata.
Tun a jiya ne kwaitin kula da gasar ya fara gudanar da zama, tare da halartar wakilan cibiyar Azhar, da kuma Sheikh Abdulfattah Tarouti da wasu daga cikin malamai.
A zaman farko da aka fara a yau, an gudanar da karatu domin tunawa da Sheikh Khalil Al-husari.
A gasar dai mahardata 52 ne daga kasashe 22 na duniya za su kara da juna, inda daga karshe za a fitar da wadanda suka fi nuna kwazo a kowane bangaren domin ba su kyautuka na musamman.