IQNA

Canada Ta Ce Za A Bi Kadun Hakkokin Musulmin Kasar China Da Ake Zalunta

22:12 - February 18, 2021
Lambar Labari: 3485666
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Canada ta sanar da cewa za a bi kadun hakkokin musulin Uighur na kasar China da ake zalunta.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau ya bayyana cewa, kasar Canada tare da wasu suna shirin daukar matakai na bin kadun hakkokin muuslmin Uighur na kasar China.

Ya ce hakika halin da wadannan mutane suk ciki abin tausayawa ne, domin ana take hakkokinsu ne na ‘yan adamtaka, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa.

Trudeau ya ce mawuyacin halin da musulmi suke ciki a kasar China ba abu ne da za a ci gaba da yin shiru a kansa ba, saboda hakan Canada da wasu kasashe sun kudiri aniyar ganin sun bi kadun wannan batu tare da majalisar dinkin duniya.

Musulmin Uighur dai sun jima suna fuskantar matsaloli da kuma matsin lamba daga gwamnatin China, bisa zarginsu da take yi da karkata ga tunani na ta’addanci.

Daga cikin irin matakan da gwamnatin China take dauka a kansu, har da tsare su wuri guda, tare da hana su fita daga yankunansu, kamar yadda kuma a kan tilasta su karya azumi a lokacin azumin watan Ramadan, da dai sauran matakai na takurawa.

3954668

 

 

 

captcha