Majiyar sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami kan kamfanin man fetur na Aramco da ke birnin Jidda na bakin tekun maliya a kasar Saudiya.
Kakakin sojojin kasar Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa, hadin guiwan sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami samfurin Quds-2 kan kayakin kamfanin Aramco na kasar Sudiya a birnin Jidda.
Kafin haka dai sojojin Yemen sun kai irin wadannan hare-hare a kan kamfanin na Aramco a cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata, inda ta jawo asarori masu yawa ga kamfanin.
Hare-Haren daukar fansar dai suna zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Saudiyya take kara tsananta hare-harenta ta sama da kasa a kan al’ummar kasar Yemen.