IQNA

23:41 - March 11, 2021
Lambar Labari: 3485735
Tehran (IQNA) jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya bayyana cewa, Alqaeeda da Daesh suna yi wa yahudawa aiki ne.

Shafin Almasirah ya bayar da rahoton cewa, a cikin jawabin da ya gabatar yau, jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen Abdulmalik Alhuthy ya bayyana cewa, Alqaeeda da Daesh suna yi wa yahudawa aiki ne wajen rusa kasashen larabawa.

Jagoran na kungiyar Ansarullah ya bayyana hakan ne ne a yau a lokacin da yake gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar Mab'ath, ranar da aka aiko manzon Allah da sakon shiriya ga dukkanin 'yan adam.

Bayan bayani kan matsayin wannan rana da kuma muhimmancinta a cikin addinin musulunci da kuma darussa da suke a cikinta, ya kuma tabo batutuwa da suka shafi siyasar yankin gabas ta tsakiya da kuma halin da ake ciki a yankin.

Dangane da ci gaba da fafatawar da ake yi a kasar Yemen da kuma yunkrin Saudiyya na ci gaba da fadada mamayarta a kan yankunan kaar Yemen a yakin da take yi da al'ummar kasar, Alhuthy ya bayyana cewa, a halin yanzu makiya al'ummar Yemen sun koma suna yin amfani da 'yan ta'addan Alqaeeda da Daesh, wadanda suu ne suke yi musu da al'ummar Yemen a yanzu.

Ya ce wadannan kungiyoyi suna yi wa makiya musulunci ne domin rusa kasashen larabawa da na musulmi.

3958986

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ansarullah ، yemen ، alqaeeda ، Daseh ، yahudawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: