IQNA

Musulmi Shi’a Da Sunnah Sun Yi Allawadai Da Yunkurin Juya Ayoyin Kur’ani Mai Tsarki A India

23:47 - March 15, 2021
1
Lambar Labari: 3485744
Tehran (IQNA) malaman mabiya mazhabobin ‘yan Sunnah da ‘yan shi’a sun yi Allawadai da yunkurin wani mutum na neman sauya ayoyin kur’ani mai tsarki a India.

Shafin yada labarai na Omid ya bayar da rahoton cewa, Wasim Razavi wani fitaccen masani musulmi a India, ya bayyana cewa ya gano cewa wasu daga cikin ayoyin kur’ani an saka su ne bayan rasuwar manzon Allah (SAW) a kan hakan ya shigar da kara a gaban kotu da ke neman a cire ayoyi 26 daga cikin kur’ani.

Wannan mutum dai ya yi da’awar cewa, dukkanin ayoyin da yake Magana a kansu suna yin kira ne ga tashin hankali da rashin zaman lafiya a tsakanin ‘yan adam, alhali kur’ani yana kira zuwa zaman lafiya ba tashin hankali ba.

Wannan batu ya fuskanci kakkausan martini daga dukkanin bangarori na malaman Sunnah da Shi’a a kasar India, inda suka fitar da bayanai na hadin gwiwa a tsakaninsu da suke kalubalantar wannan mutum, tare da kalamin nasa a matsayin ridda daga addinin musulunci, saboda ya musunta ayoyin kur’ani saboda ra’ayinsa.

Bayanan hadin gwiwa da dukkanin malaman na Sunnah da Shi’a suka fitar a kasar India, sun tabbatar da cewa kur’ani mai tsarki kammalallen littafi ne daga Allah madaukakin sarki, kuma dukkanin musulmi sun yi Imani da cewa dukkan ayoyin da suke cikinsa an saukar da su ne ga manzon Allah (SAW).

Kamar yadda suka jaddada cewa taba martabar kur’ani mai tsarki yana matsayin taba martbar addinin mulunci ne da dukkanin muusulmi na duniya baki daya.

Dubban musulmi ne a sassa na kasar India suka gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da wannan kalami, tare da nisanta kansu daga gare shi.

3959547

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Hajia
0
0
Allah yakyauta
captcha