IQNA

Babban Malami Mai Bayar Da Fatawa Na Uganda Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa

12:09 - April 06, 2021
Lambar Labari: 3485787
Tehran (IQNA) Sheikh Sulaiman Indirankuwa babban malami mai bayar da fatawa ga musulmin kasar Uganda ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa.

Wannan mataki na zuwa ne sakamakon wasu matsaloli da kuma rashin fahimtar juna tsakanin Sheikh Sulaiman Indirankuwa da wasu manya daga cikin majalisar musulmin kasar, wanda ya fito ya sanar a cikin wani bayani da ya yi a gidan talabijin.

Kafin wannan lokacin dai an gudanar da janazar daya daga cikin manyan fitattun musulmin kasar ta Uganda a wannan mako, amma sabanin yadda aka saba Sheikh Sulaiman Indirankuwa bai gabatar dabayani a wurin jana’izar ba.

Malamin dai ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin kauce wa duk wani abin dai zai iya kawo sabani tsakanin al’ummar musulmi na kasar Uganda, wanda hakan ko kadan ba maslaha ce ga kowa ba.

Haka nan kuma yi fatan ganin cewa duk wanda zai karbi mukami ya samu nasara wajen gudanar da abin da zai ciyar da musulunci a gaba a kasar Uganda, kamar yadda ya jaddada cewa zai bayar da dukkanin goyon bayansa ga duk wanda aka mika wa wannan mukami nasa da ya yi murabus daga kansa.

A nasa bangaren shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da matakin da Sheikh Sulaiman Indirankuwa ya dauka na yin murabus daga kan mukaminsa, inda ya bayyana cewa mutum ne mai son ganin an samu ci gaba da zaman lafiya da fahimtar juna a dukkanin fuskoki tsakanin dukkanin mabiya addinai na kasar Uganda.

3962717

 

captcha