IQNA

Za A Sake Bude Wani Masallaci Da Gwamnatin Faransa Ta Rufe A Baya

8:55 - April 08, 2021
Lambar Labari: 3485793
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Faransa tana shirin sake bude wani masallacin musulmi da ta rufe a lokutan baya.

Shafin yada labarai na arabi 24 ya bayar da rahoton cewa, yanzu haka  gwamnatin kasar Faransa tana shirin sake bude wani masallacin musulmi da ta rufe a lokutan baya, biyo bayan kisan da wani dalibi ya yi wa malaminsa, sakamakon cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Kafin wannn lokacin gwamnatin Faransa ta bayyana cewa, ta dauki matakin rufe wannan masallaci ne a ranar 21 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, kuma za a bude masallacin ne bisa sharadin cewa dole nea  canja limamin masallacin wanda ta kira da mai tsatsauran ra'ayi.

Gwamnatin ta yi zargin cewa an yada wani bayania  shafin facebook daga wannan masallaci ne wanda a cewarta, hakan ya tunzura yaron da ya yi kisan.

Baya ga haka ma gwamnatin Faransa ta rufe wasu masallatai a fadin kasar, bisa zargin cewa suna yada ayyukan ta'addanci, tun bayan watsa zane-zanen batunci da jaridar kasar ta yi a kan manzon Allah, ba tare da yin Allawadai da abin da jaridar take aikatawa ba.

3963124

 

 

 

 

 

captcha